Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Matukin kwale-kwalen da kuma wasu mata biyar sun tsira daga mutuwa a yayin da abin hawan nasu ya yi kulikulin kubura.
Matan da su ka rasa rayukan nasu, leburori ne da suke aikatau a gonakin da suke yankin Souki, kuma suna komawa gida ne a lokacin da hatsarin ya faru.
Tekun na “ Blue-Nile” dai yana da muhimmanci ta bangaren kasuwanci, inda yake isa birnin Khartum sannan kma yake hadewa da tekun maliya.
A shekarar 2018 ma an sami wani hatsari irin wannan da dalibai 22 su ka nitse a cikin jirgin ruwa.
342/