12 Maris 2022 - 13:39
Tattaunawar Abdolahian Da Borrell Ta Yi Armashi

Ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir Abdollahian, ya bayyana tattaunawarsa da shugaban kula da manufofin ketare na kasashen turai, Joseph Borrell, da cewa ta yi armashi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A zantawar ta wayar tarho data wakana jiya bangarorin biyu sun tabo halin da ake ciki game da tattaunawar da ake a Vienna, a yunkurin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Yayin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa, bai kamata mahimman batutuwa kan dage takunkumi a rika amfani da matsin lamba akansu ba daga bangaren Amurka.

A cewar AmirAbdollahian, ana ci gaba da kokarin ganin an cimma yarjejeniyar mai kyau wacce kuma zata dorewa.

A ranar 27 ga watan Disamban bara ne bangarorin da yarjejeniyar ta kunsa da suka hada da Rasha, Sin, Faransa, Biritaniya da kuma Jamus suka koma bakin tattaunawar ta Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a 2015.

342/