4 Janairu 2022 - 14:14
Murtaniya : Shugaba Mohamed Ould Sheikh El-Ghazwani Ya Kamu Da Cutar Corona

A yau Talata, fadar shugaban kasar Mauritaniya ta sanar da cewa shugaban kasar Mohamed Ould Sheikh Al-Ghazwani ya kamu da cutar ta Corona, inda ta yi nuni da cewa yana fama da kananan alamu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa an yi wa shugaba Ould Sheikh El-Ghazwany gwaje-gwaje ne bayan ya kamu da mura, kuma gwajin da aka yi ya nuna cewa ya kamu da cutar Corona.

A baya-bayan nan dai kasar Mauritania ta fuskanci karuwar kamuwa da cutar ta corona. Kuma kasar Mauritaniya ta yanke shawarar rufe filayen wasanni ga jama'a saboda barkewar cutar Corona, da kuma kokarin kaucewa ci gaba da yaduwarta a fadin kasar.

342/