4 Janairu 2022 - 14:11
​Ana Ci Gaba Da Kira Ga Shugaban Somalia Da Firaministansa Su Kai Zuciya Nesa

Kasashen duniya na ci gaba da kira ga shugaban Somalia da firaministansa akan su kai zuciya nesa, a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar takun tsaka tsakanin manyan jami’an biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dangantaka tsakanin bangarorin biyu ta yi Kamari ne tun bayan da shugaba Farmajo ya yi yunkurin korar firaministansa Mohamed Hussein Roble.

Shugaban dai na mai zargin firaministansa da hadassa tsaiko ga shirya zabubukan kasar da suka fuskanci jinkiri na tsawon watanni, da kuma cin hanci da rashawa.

Shi kuwa a nasa bangaren firaministan kasar, na mai zargin shugaban aksar da neman mallakewa kan madafun iko.

A halin da ake ciki dai firaministan ya sanar da kafa wani kwamitin ministoci mai yaunin gudanar da bincike kan yunkurin kifar da shi daga mukaminsa, a yayin da ‘yan adawa a kasar ke kira ga shugaban kasa da ya yi murabus.

Babban abun damuwa a kasar shi ne yadda dukkan bangarorin ke samun goyan bayan daga bangaren jami’an tsaro.

Kasashen duniya da dama sun nuna damuwa akan halin da ake ciki yayin da suke kiran a kai zuciya nesa, ta hanyar warware rikicin aksar ta hanyar siyasa.

342/