3 Janairu 2022 - 16:45
Iran: A Yau Litinin Ce Ake Komawa Kan Teburin Tattaunawar Daukewa Iran Takunkuman Tattalin Arziki

A yau litinin ce za’a sake komawa kan teburin tattaunawa don daukewa kasar Iran takunkuman tattalin arziki a birnin Vienna na kasar Austria bayan hotu na kwanaki uku saboda shigowar sabuwar shekara ta 2022.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - na kasar Iran ya nakalto Ali Bakiri-Kani shugaban tawagar Iran a tattaunawar yana cewa sun ci gaba da musayar ra’ayi a cikin hutun, tsakanin mahalatta taron na Vienna.

Kani ya kara da cewa an sami ci gaba so sai a cikin bangarori 4 wadanda kasashen 4+1 da kuma Iran suke tattaunawa a zagaye na 8 na tattaunawar daukewa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.

Daga karshe Bakiri-Kani ya kammala da cewa a halin yanzu tattaunawar tana maida hankali ne kan abubu hudu wadanda suka hada da dagewa Iran takunnkuman tattalin arzikin da Amurka ta dora mata, bata damar tabbatar da cewa an dauke su, komawa kan yarjejeniyar JCPOA da kuma lamuni kan cewa ba wani bangaren da zai sake ficewa daga yarjejeniyar.

342/