Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan bayanin ya fito ne bayan ziyarar gaggawa da mai shiga Tsakani na kungiyar kan batun Mali kana tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya kai a Bamako a farkon wannan mako inda ya gana da shugaban mulkin sojin na Mali, Kanal Assimi Goiti.
Mistan Jonathan, ya ziyarci hukumomin Malin ne tare da shugaban kwamitin kungiyar ta Ecowas.
Ziyarar jami’an biyu sako ne da taron shugabanni da gwamnatocin kungiyar ta Ecowas, ya aike wa sojojin dake rike da mulki a Mali, na ganin cewa sun gudanar da zabe kamar yadda aka shirya a karshen watan Fabarairu a Mali, wanda kuma Ecowas ke bukatar jadawalin zaben dalla dalla kafin nan da karshen wannan shekara.
Saidai har yanzu babu bayyanai daga sojojin dake rike da mulki a Malin kan wannan bukata ta Ecowas, saidai a kwanakin baya gwamnatin rikon kwaryar Malin ta ce tana bukatar Karin lokaci ta yadda za ta kimsa zaben duba da jerin matsalolin da kasar ke fama da su, wadanda ba zasu bada damar gudanar da zabe ba.
Baya ga hakan ma hukumomin Malin na son gudanar da taron shawarwari na kasa kafin fitar da jadawalin zaben.
342/