Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A yayin zagayowar makon littafai a kasar Iran, kasar ta taimaka ma makarantun addini na Uganda da litattafai da suka shafi addini, al'adu, tarihi, a matakai daban-daban na matasa da manya, wanda aka bayar ga makarantun Islamiyya.
Daga cikin littafan akwai mujalladai na fassarar littafan Shahid Morteza Motahhari a cikin harshen mutanen Uganda, da kuma littafan ilmomi daban-daban, wadanda wasunsu an fassara su a cikin harshen mutanen kasar.
Duk wannan yana daga cikin kyautukan da cibiyar yada al'adu da ilimin musulunci ta kasar Iran ta dauki nauyin bayarwa ga makarantun.
Kasar Iran dai tana da kyakkayawar dangantaka da kasar Uganda, kamar yadda kuma musulmin kasar suke da kyakkyawar alaka da kasar Iran, wadda take taimaka musu a bangarori daban-daban, musamman wajen gina masallatai da cibiyoyi da makarantu na addini har da na boko.
342/