20 Nuwamba 2021 - 14:45
Guinea: Sojoji Sun Yi Alkawalin Mika Mulki Ga Farar Hula

Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar Guinea Mamady Doumbouya wanda ya gudanar da taron farko da ministocinsa ya jaddada aniyar gwamnatin na mika wa fararen hula mulki a cikin ruwan sanyi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shi kuwa fira ministan rikon kwarya na gwamnatin rikon kwaryar ta kasar Guinea Muhammad Beavogui ya ce’; Za a mika mulki ne a cikin kankanin lokaci, kuma za a yi kyakkyawan tsari domin gina ginshiki mai karfi na cigaban kasar.

Har ila yau fira ministan ya ce; Yana sane da cewa takaitaccen aikin da yake a gabansu shi ne gudanar da gwamnatin rikon kwarya, ba gudar da manyan ayyuka na raya kasa ba.

A cikin watan Oktoba day a gabata ne dai Mamady ya jagoranci kifar da gwamnatin shugaba Conde dan shekaru 83.

Conde ya sauya kundin tsarin mulkin kasar saboda ya bai wa kansa damar yin zango na uku na shugabancin kasar, lamarin da ya jawo masa fushin al’ummar kasar.

342/