13 Nuwamba 2021 - 16:26
​Iran: Za’a Fara Tattaunawar Vienna Ne Daga Batun Daukewa Iran Takunkuman Tattalin Arziki

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren siyasa Ali Bakiri ya bayyana cewa batun daukewa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dora mata ne za’a fara magana a kansa, a tattaunawar Vienna mai zuwa a karshen wannan watan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : kasar Iran ya nakalto Bakiri ya na fadar haka a dai dai lokacinda tattaunawar Vienne ke karatuwa. Dangane da bukatar kasashen yamma na a fara tattaunawar ta Vienna daga inda aka tsaya a tattaunawar karshe, Bakiri ya ce, babbar matsala a wajen Iran itace takunkuman da Amurka ta dorawa kasar, da kuma matsalolin da ficewar Amurka ya jawowa yarjejeniyar JCPOA.

Ali Bakiri ya kammala da cewa Amurka ce ta fice daga yarjejeniyar, Iran tana cikinta, don haka abu na farko da Amurka za ta yi idan tana son dawowa cikin yarjejeniyar, shi ne ta dage wadannan takunkuman da ta dorawa Iran, sannan sai Iran ta tabbatar an dage takunkuman da gaske, sanann ta koma inda take kafin ficewar Amurka.

342/