Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Hossein Amir-Abdollahian ya bayyana cewa: "Fadar White House ta yi kira da a yi shawarwari da Iran tare da ikirarin cewa a shirye ta ke ta koma cikin yarjeejniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a 2015, amma duk da haka a lokaci guda ta kakaba wasu sabbin takunkumai akan daidaikun mutane da hukumomin Iran."
A don haka a cewarsa "Muna nazarin halin Mr. Biden sosai,"
Ya nanata cewa, manufar tattaunawar ba wai magana ce kawai ba, a'a don cimma sakamako mai amfani da moriyar juna ne.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi nuni da cewa, ya kamata kasashen turai da suka rage a yarjejeniyar su kasance a shirye don yin shawarwari ta yadda kowa zai amfana.
342/