Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kakakin asusun na Unicef ne, ya bayyana hakan bayan komawarsa a Geneva, bayan ya ziyarci kasra ta Yemen.
James Elder, ya ce, rikicin Yemen ya kai wani mataki da za’a dangantawa da abun kunya, inda tun bayan barkewarsa yara 10,000 aka kashe ko aka lahanta daga watan Maris ne shekarar 2015 zuwa yanzu.
Hakan kwatankwacin yaro hudu ne da wannan lamari ke shafa a ko wacce rana, inji kakakin asusun na Unicef James Elder.
342/