29 Satumba 2021 - 15:41
Faransa Ta Tsaurara Matakan Bada Visa Ga Kasashen Larabawan Magreb

Kasar Faransa ta tsaurara matakan bada takardar shiga kasar ta Visa, ga ‘yan kasashen Morocco, Aljeriya da kuma Tunisia.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Gidan talabijin na Europe1, wanda ya samu tabbacin labarin daga kakakin gwamnatin kasar, Gabriel Attal, ya ce faransa ta dauki wannan matakin ne duba da matsalolin da take fuskanta wajen mayar da wasu ‘yan daga cikin ‘yan kasashen gida daga kasar.

A don haka faransa ta dauki matakian rage bada visa ga ‘yan kasashen da kashi hamsin cikin dari ga ‘yan Aljeriya da Morocco, sai kuma kashi talatin cikin dari ga ‘yan kasar Tunisia.

Faransa ta ce bayan amfani da matakin diflomatsiya da baranaza, ba tare da shayo kan lamarin ba, hakan ya sa ta yi amfani da takunkumi.

Tuni dai kasashen Aljeriya da Morocco, sukayi tir da matakin wanda suka ce bashi da wani dalili, sannan ba kamshin gaski a ciki.

342/