Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Sojojin HKI sun kai wani samame na kokarin kama fursunoni falasdinawa guda 6 da suka tsere daga gidan yarin Gilboa a ranar litinin da ta gabata, duk da tsananin tsaro da ake bawa gidan yarin, wanda ake daukar sa a matsayin gidan yari mafi tsaro a Isra’ila
A wani taron manema labarai da kungiyar ta Jihadil islami ta kira ta fadi cewa Idan sojojin Isra’ila suka kuskura suka shiga birnin Jenin to za su fuskanci turjiya da karfin manyan makamai , kuma ta ce za ta mayar da martani mai zafi idan aka samu wani canji kan Fursunoni palasdinawa da ke gidan Yarin Isra’ila domin jikkata duk wani bafalasdine guda daya jan layi ne gareta.
342/