ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto ministan kiwon lafiya na kasar Iran, ya na cewa, an yiwa mutane 646,732 alluran riga kafin cutar Covid 19 a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata.
Wanda ya kawo adadin wadanda aka yi wa alluran riga kafin zagaye na farko zuwa 13,520,127, sannan wadanda aka yi wa zagaye na biyu kuma zuwa 3,274,980.
Gaba daya dai mutane 16,795,107 ne aka yi wa alluran raga kafin ya zuwa yanzu. A cikin sa’o’ii 24 da suka gabata dai mutane 39,139 suka kamu da cutar ta Covid 19 a duk fadin kasar, sannan 4,636 daga cikinsu suna jinya a asbitocin kasar, a yayinda wasu 508 kuma suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar.
342/