24 Yuli 2021 - 06:20
​Shugaban Kasar Faransa Ya Canza Waya Da Kuma Lambar Wayarsa Saboda Rahoton Leken Asirin Da Isar’ila Take Yi

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya canza waya da kuma lambar wayarsa bayan rahotannin da suka tabbatar da cewa gwamnatin haramtacciyarkasar Isra’ila (HKI) ta na satar sauraron maganganun shuwagabannin kasashen duniya da dama.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin fadar Elesee, Gabriel Attal ya na cewa, shugaban ya dauki wannan matakin ne bayan wani taron gaggawan da ya gudanar tare da majalisar ministocinsa a jiya Alhamis dangane manhajar ‘Pegasus na satar bayanai’ wanda gwamnatin HKI, tare da taimakon wasu kamfanonin sadarwa na wasu duniya take satar jin abubuwan da wasu shuwagabannin suke tattaunawa ta wayoyinsu.

Gabriel Attal ya ce rahotanni sun bayyana cewa HKI ta na satar jin magana a wayoyin shugaba macron da na wasu ministocinsa tare da amfani da wannan manhajar.

Rahotannin sun bayyana cewa jami’an tsaro a kasar Morocco sun yi amfani da wannan manhajar wacce HKI ta samar inda ta taimaka HKI satar jin maganar shugaba Macron da wasu minsitocinsa.

Amma gwamnatin kasar Morocco ta musanta zargin. A halin yanzu dai gwamnatin Faransa ta bude bincike don tabbatar da gaskiyar abinda ya faru.

342/