16 Yuni 2021 - 13:21
Кungiyoyin Kare Haƙƙoƙin Bil’adama Na Кasa Da Кasa Sun Yi Tir Da Kashe Saurayi Ɗan Shi’a Da Saudiyya Ta Yi

Кungiyoyin kare haƙƙoƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa, ciki kuwa har da ƙungiyar nan ta Amnesty International, sun yi tir da ƙasar Saudiyya saboda zartar da hukuncin kisa kan wani saurayi ɗan Shi’a bisa zargin bore wa gwamnati alhali a lokacin yana ɗan ƙaramin yaro.

ABNA24 : A jiya Talata ne dai gwamnatin Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa a kan Mustafa bin Hashem bin Issa al Darwish, saurayin da ya fito daga yankin Qatif da mafiya yawan mazauna wajen ‘yan Shi’a ne.

Mahukuntan Saudiyyan dai sun zargi Mustafa ɗin ne da laifin ɗaukar makami don yaƙar masarautar, barazana ga tsaron ƙasa, ƙirƙirar ƙungiyar ta’addanci da nufin kasha jami’an tsaro da kuma tunzurawa don yin bore, bisa hakan ne wata kotu a Saudiyya ta yanke masa hukuncin kisar da aka zartar a jiyan.

Кungiyoyin kare haƙƙoƙin bil’adaman dai sun ce ba a yi wa matashin adalci ba yayin shari’ar bisa la’akari da cewa an tilasta masa ne amincewa da zargin da ake masa sannan kuma lokacin da aka kama shi bisa wannan laifin yana ƙasa da shekaru 17 ne, kamar yadda kuma suka yi zargin cewa tsawon lokacin da ake tsare da shi jami’an tsaron Saudiyyan sun ɗanɗana masa nau’oi daban-daban na azaba.

Iyayen matashin dai sun ce ba a sanar da su za a zartar da wannan hukuncin ba, su ma ta kafafen watsa labarai suka sami labari.

Кungiyoyin kare haƙƙoƙin bil’adaman sun ce zartar da wannan hukuncin yana nuni da cewa har ya zuwa yanzu Saudiyya ba da gaske take yi ba a ikirarin da Yarima mai jiran gado na ƙasar yake yi na haifar da sauyi a ƙasar.

Tun a shekara ta 2011 ne dai yankin gabashin ƙasar Saudiyyan ya ke fama da zanga-zangogi na lumana inda mutane suke buƙatar sauyi, ‘yancin faɗin albarkacin baki, sako fursunoni na siyasa da ake tsare da su bugu da ƙari kan kawo ƙarshe nuna wariya na addini da tattalin arziki da ake yi wa mutanen yankin waɗanda mafi yawansu ‘yan Shi’a ne, to sai dai kuma mahukuntan Saudiyya suna ci gaba da amfani da ƙarfin tuwo wajen kawo ƙarshen wannan nuna rashin amincewar.

342/