ABNA24 : Wata sanarwa da ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar ta fitar, ta ce an dau wannan matakin ne duba da yadda ake fuskantar sabbin nau’ukan cutar a kasashen duniya da dama da kuma sake dawowan cutar mai tsanani a karo na uku.
A don haka za’ayi wa mutanen kasar ‘yan tsakanin shekara 18 zuwa sama riga kafin cutar kama daga ma’aikata na gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu, da jami’an tsaro da kuma ma’aikatan tashohin mota dana sufirin jiragen sama.
Ministan lafiya na kasar Dakta Illiasu Idi mai Nassara, ya sake nanata cewa, yin riga kafin shi ne kawai mafiya na kaucewa yaduwar cutar musamman sabbin nau’ukan dake yaduwa a duniya.
Jamhuriyar Nijar dai ba ta daga cikin kasashen dake fuskantar yawan masu kamuwa da cutar, saidai hukumomin kasar sun ce hakan baya nufin a yi watsi da matakan da ake dauka na yaki da annobar, ciki har da yin alluarn riga kafin.
Alkalumman da ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar ta fitar a ranar 14 ga watan nan sun nuna cewa, mutum 5452 ne suka kamu da cutar a fadin kasar tun bayan bullarta, sai kuma 192 da cutar ta yi ajalinsu.
342/