ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto majiyar kungiyar tarayar Turai ta na fadar haka a jiya Talata. Majiyar ta kara da cewa Abbas Araqchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ne zai jagoranci tawagar iran a tattaunawar ta yau. A yayinda mataimakin Jami’i mai kula da al’amuran harkokin waje na tarayyar Turan, wato Mr Enrique Mora ne zai jagoranci taron gaba daya.
Ana saran wakilai daga kasashen Rasha Cana, Faransa da Burtania ne zasu halatci taron tattauna hanyoyi farfado da yarjejeniyar ta JCPOA.
Iran dai ta dage kan cewa sai an dage mata dukkan takunkuman tattalin arziki wadanda tsohuwar gwamnatin AMurka ta dorawa kasarsa bayan ficcewarta daga yarjejeniyar ta JCPOA kafin ta dawo kan yarjejeniyar.
342/