ABNA24 : Yana da kyau kowa da kowa ya kiyaye irin matakan da hukumomin kiwan lafiya suka gindaya domin kaucewa kara yaduwar cutar korona, inji shugaba Ruhanin.
Nan da mako guda ne za’a shiga sabuwar shekara ta 1400 hijira shamsiyya, ta kalandar da Iraniyawa ke amfani da ita, kuma yayin bikin sabuwar shekarar iraniyawa kan ziyarci ‘yan uwa da abokan arziki a garuruwa da kyauyukansu
Saidai a cewar shugaba Ruhanin, ya kamata jama’a su kiyaye sosai, domin kada a fuskanci sake dawowar cutar.
342/