ABNA24 : A cikin wani rahoton jaridar Premium Times ta bayyana cewa, shugaban Kwamitin Sayar da Kadarorin, Dayo Apata, ya jagoranci tawagar domin ganin wasu daga cikin gidajen da kuma kadarorin a wurare hudu a cikin birnin Abuja.
Apata, wanda ke jagorancin kwamitin, Babban Lauya ne a Ma’aikatar Shari’a, Ya sheda da wa manema labarai cewa an bai wa kwamitinsa damar sayar da kadarorin, wadanda suka hada da maka-makan gidaje, masana’antu, manyan motocin alfarma, da dai sauransu.
Bayan haka kuma akwai kananan jiragen ruwa, da kuma bababn jirgin ruwa gami da sarkoki na gwala-gwalai, wanda kuma har yanzu kwamitin yana ci gaba da karbar lissafi na wadanan kaddarori daga hukumar EFCC, wadanda ta kwato daga hannun barayin gwamnati.
Hukumar ta EFFC dai ta kwace wadannan kaddarori ne daga hannun mutanen da ake zargin sun wawuri dukiyar al’ummar kasa, sun yi sama da fadi da ita, tare da azurta kansu da iyakansu.
342/