ABNA24 : Har ila yau, ya kuma yi wa al’ummar kasar ta Lebanon jawabi da a ciki ya nemi gafararsu akan kasawarsa ta kafa sabuwar gwamnatin, yana mai ci gaba da cewa; Wajibi ne a ci gaba da aiki da shirin da shugaban kasar Faransa ya kaddamar da shi, saboda yana kunshe da kyakkyawar niyya.
Jam’iyyar shugaban kasar ta Lebanon “Tayyarul Wadhniyyul-Hur’ ta bayyana cewa; tana ci gaba da riko da shirin da shugaban kasar Faransa ya gabatar da shi da zai kai ga kafa gwamnati saboda a yi gyare-gyare a tsarin siyasar kasar.
Shi kuwa babban muftin ja’afari na kasar Lebanon Ahmad Kublan ya bayyana cewa; Janyewar da Adib ya yi, matsala ce gagaruma wacce kuma take rusa shirin na kasar Faransa.
342/