3 Satumba 2020 - 10:50
Zarif; Mun Daura Damarar Dakile Yunkurin Makiya

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa; Ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare manufofin kasarmu, kuma ni da abokan aikina a ma’aikatar harkokin wajen da kuma dukkanin jami’an diplomasiyyar Iran, muna aiki dare da rana, domin dakile duk wani yunkuri na Trump da ‘yan sahayoniya.

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana haka ne a yau Laraba da yake ganawa da ‘yan jarida, inda ya kara da cewa;A daidai wannan lokacin da gwamnatin Trump da HKI su ke zage damtse domin kara matsin lamba na tattalin arziki da tsaro akan jamhuriyar musulunci ta Iran, ni da abokan aikina a ma’aikatar harkokin waje da kuma ofisoshin jakadanci muna aiki dare da rana domin dakile wannan kokarin nasu.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da nasarori uku na diplomasiyya da Iran din ta samu akan Amurka a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a cikin makwannin bayan nan.

342/