4 Agusta 2020 - 12:12
Lebanon : An Nada Charbel Wehbe A Matsayin Sabon Ministan Harkokin Waje

A Lebanon sa'o'i kadan bayan da ministan harkokin wajen kasar Nassif Hitti ya yi murabus, shugaba Michel Aoun ya nada Charbel Wehbe a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar.

ABNA: Kafin a damka masa wannan matsayin, Charbel Wehbé, shi ne mashawarcin shugaban kasar kan harkokin diflomatisyya.

A jiya ne dai ministan harkokin wajen kasar, Nassif Hitti, ya mika takardar murabus dinsa, saboda a cewarsa halin da kasar kan iya fadawa sakamakon matsalar tattalin arziki.

Babban jami'in diflomasiyyan ya zama ministan harkokin waje ne a watan Janairu a gwamnatin Fira Mmnista Hassan Diab.

Saidai wasu rahotanni na daban sun ce, M.Hitti ya shiga yanayi na takaici ne sanadiyyar sukar da Diab ya yi ga Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian, yayin wata ziyara da jami’in diplomasiyyan na Faransa ya kai Beirut a kwanan nan.

342/