ABNA24: Saidai a bana maniyata kimanin dubu ne zasu shiga aikin hajjin na bana sakamakon annobar cutar korona wacce ta dagula al’amura a duniya baki daya, kuma an dau wannan matakin ne domin kare lafiyar alhazai.
Kafin hakan dama ma'aikatar cikin gidan Saudiyyar, ta bayyana a ranar Lahadi cewa, ta kammala dukkanin shirye shirye, na gudanar da Hajjin bana cikin nasara.
Daga cikin maniyyata aikin Hajjin na bana, akwai Alhazai 'yan kasashe 160, ciki hadda mutum 70 'yan kasashen waje dake zaune a cikin kasar.
Kaza lika, an tanaji hukuncin dauri, da biyan tara ga duk dan kasa da ya karya ka'idojin da aka gindaya, na tsaron lafiyar maniyyatan, za kuma a tusa keyar duk wani bako dan kasar waje da ya karya dokokin zuwa gida.
A Alkalumman ranar Lahadi da ma'aikatar lafiyar Saudiyya ta fitar, mutum 250,920 suka harbu da cutar sai kuma 2,486 da cutar ta yi ajalinsu a daukacin fadin kasar.
342/