(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa wakilan gamayyar jam’iyyun sun bukaci a kafa kwamiti na musamman wanda zai rika bin duddugin inda aka kwana kan shigar da karar.
Daga karshe majalisar dokokin kasar ta Iraqi ta yaba da yin allawadai da hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya ta yi na kashe Janar Qasim Sulaimani wanda gwamnatin kasar Amurka ta yi a farkon wannan shekara.
A ranar 3 ga watan Jenerun wannan shekara ne dai, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada umurnin kashe Janar Kasim Sulaimani kwamandan rundunar Qudus ta JMI tare da Abu Mahdi Almuhandis da kuma wasu mutane 8 tare da su a tashar jiragen sama na birnin Bagdaza na kasar Iraqi.
342/