21 Yuni 2020 - 08:14
Libya: Gwamnatin Tripoli Ta Yi Watsi Da Kiran Masar Na Gudanar Da Zama Kan Rikicin Libya

Gwamnatin Tripoli ta yi watsi da kiran da gwamnatin kasar Masar ta yi na neman kungiyar kasashen larabawa ta gudanar da zaman gaggawa kan rikicin kasar Libya.

(ABNA24.com) Gwamnatin Tripoli ta yi watsi da kiran da gwamnatin kasar Masar ta yi na neman kungiyar kasashen larabawa ta gudanar da zaman gaggawa kan rikicin kasar Libya.

Tashar talabijin ta RT ta bayar da rahoton cewa, Jaridar Al-wasat ta kasar Libya ta bayar da rahoto a bugunta na yau Asabar cewa, ministan harkokin wajen gwamnatin Tripoli Muhammad Tahir ya sanar da cewa, ba za su amsa kiran da gwamnatin Masar ta yi ba, na neman majalisar kasashen larabawa ta gudanar da zaman gaggawa kan rikicin kasar Libya.

A cikin bayanin nasa, ministan harkokin wajen gwamnatin Tripoli ya bayyana cewa, ya sanar da babban jami’i mai kula da harkokin gudanar na kungiyar kasashen larabawa dangane da matsayin nasu.

Kafin wannan lokacin dai babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Husam Zakiy ya sanar da cewa, gwamnatin Masar ta tuntube shi kan gudanar da zaman gaggawa na dukkanin kasashen larabawa, tare da halartar ministocin harkokin wajen kasashen, domin tattauna batun rikicin kasar Libya.


/129