14 Yuni 2020 - 09:30

​Iran Ta Mayar Da Martani Kan Rahoton MDD Dangane Da Harin Aramco

(ABNA24.com) Tawagar kasar Iran a majalisar dinkin duniya ta mayar da martani dangane da rahoton da babban sakataren majalisar dinkin duniya ya gabatar, a kan harin da aka kaddamar a kan kamfanin mai na Aramco da kuma makaman da aka yi amfani da su wajen kai harin.

A cikin martanin na Iran wanda jakadan Iran a majalisar dinkin duniya Majid Takhr Ravanchi ya fitar, ya bayyana cewa abin ban takaici ne yadda majalisar dinkin duniya ta fada tarko na siyasa maimakon aiki na kwarewa a bangaren diflomasiyya.

Bayanin ya ce bincike irin wannan na bukatar aiki ne na kwararru masana, kuma aikin nasu ya zama cikin ‘yanci, ba karkashin matsin lamba na siyasa ba, ko kuma kwadaitar da su da daloli domin su fitar da sakamakon da wani bangare ke bukata, domin cimma manufi na siyasa a kan wani banagren.

A cikin rahoton da babban sakataren majalisar dinkin duniya ya gabatar bayan harin ramuwar gayya da mayakan kasar Yemen suka kaddamar kan kamfanin main a Aramco a kasar Saudiyya a shekarar da ta gabata, ya bayyana cewa; an samu wasu tarkacen makamai masu linzami da kuma jiragen yaki marassa matuki wadanda aka kera bangarorinsu a Iran, wanda hakan a cewarsa ya sabawa kudirin MDD mai lamba 2231 a kan shirin Iran an nukiliya.

Bayanin na Iran ya ce bincike na kwararu baya dogaro da zato, yana dogaro ne da kwakkwarar hujja ta zahiri, wadda rahoton kuma bai gabatar da ita ba, illa dai ya kwatanta wasu baraguzan makaman ne da wasu makamai da sojojin Iran suke nunawa a lokacin maci na soji, wanda kuma bisa doka taka da kasa wannan ba hujja ba ce.


/129