26 Mayu 2020 - 07:14
Iran Tayi Tir Da Tsoma Baki Kan Kasar China

Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Duk Wani Matakin Tsoma Baki A Harkokin Da Suka Shafi Cikin Gidan Kasar China.

(ABNA24.com) A jawabin da ya fitar a jiya Lahadi: Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Musawi ya bayyana cewar rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan wata kasa da kiyaye hurumin kasar na ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya gami da mutunta jagorancin kowace kasa a duniya, yana daga cikin tushen dokokin kasa da kasa, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana nan a kan wannan tsari don haka ba za ta taba canza siyasarta kan haka ba.

Abbas Musawi ya kara da jaddada cewa: A bisa dokokin kasa da kasa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana jaddada bukatar ganin an girmama hurumin kasar China a matsayin kasa daya dunkulalliya, kuma tana yin Allah wadai da tsoma bakin duk wata kasa a harkokin da suka shafi kasar China musamman duk wani abin da zai shafi jagorancinta tare da jaddada aiwatar da dokoki da tsarin gudanarwa da zai kai ga wanzar da zaman lafiya da tsaron al’ummar yankin Hong Kong.


/129