12 Mayu 2020 - 08:05
​Iran: Mutane 19 Sun Rasa Rayukansu A Wani Hatsari Da Ya Auku Yayin Atisayin Soji

Majiyoyin rundunar sojin kasar Iran sun sanar da cewa, a jiya an samu wani hadari a yayin gudanar da wani atisayi da sojojin kasar Iran suke yi a cikin tekun Oman, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 tare da jikkatar wasu 15.

(ABNA24.com) Majiyoyin rundunar sojin kasar Iran sun sanar da cewa, a jiya an samu wani hadari a yayin gudanar da wani atisayi da sojojin kasar Iran suke yi a cikin tekun Oman, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 tare da jikkatar wasu 15.

Kamfanin dillancin labaran FARS ya bayar da rahoton cewa, bisa sanarwar da rundunar sojin kasar ta Iran ta bayar, hadarin ya faru ne bayan harba makami mai linzami bisa kure da daya daga cikin manyan jiragen yakin kasar Iran ya yi a yayin atisayin, wanda ya samu daya daga cikin jiragen ruwa na yaki da ke cikin atisayin bisa kure.

Bayanin ya ce jirgin da makamin ya samu samfurin Kenarak, yana gudanar da ayyukan kai taimako ne ga sauran jiragen ruwa na yaki na Iran da suke cikin atisayin.

Rundunar sojin Iran ta ce tana gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru, kafin ta fitar da cikakken bayani a hukumance.



/129