(ABNA24.com) Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, ya goyi bayan takarar tsohon mataimakinsa, Joe Biden, a zaben shugabancin kasar Amurka dake tafe.
M. Obama, wanda ke bayyana goyan bayansa ga M. Biden, ta kafar bidiyo, ya bayyana cewa zabar da ya yi wa Joe Biden a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya kasance daya daga cikin matakai mafi kyau da ya dauka, kuma yana da dukkan halayen da muke son gani ga wani shugaba a yanzu.
Goyan bayan ba Obama ga Biden na zuwa ne kwanaki kadan bayan da sanata, Bernie Sanders, ya janye takararsa dage zaben fidda gwani na jam’iyyar ‘yan demokrate.
Tsohon shugaban kasar ta Amurka, Barack Obama, ya kuma nemi hadin kan a jam’iyyar ta demokrate tare da yabawa da halayen dukkan ‘yan takaren fidda gwani na jam’iyyar.
A Amurka har yanzu Barack Obama na da farin jinni wajen ‘yan kasar, a cikin minti arba’in da wallafa bidiyonsa a shafin twitter an kale shi fiye da sau miliyan daya.
/129
16 Afirilu 2020 - 04:59
Lambar labari: 1026288
Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, ya goyi bayan takarar tsohon mataimakinsa, Joe Biden, a zaben shugabancin kasar Amurka dake tafe.