8 Afirilu 2020 - 07:25
​Corona Ta Kashe Mutane Akalla 6,159 A Kasar Burtaniya

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Burtaniya ta sanar a yau cewa, adadin mutanen da suka mutu a kasar sanadiyyar kamuwa da cutar coron ya kai 6,159, bayan mutuwar wasu mutane 758 a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata.

(ABNA24.com) Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Burtaniya ta sanar a yau cewa, adadin mutanen da suka mutu a kasar sanadiyyar kamuwa da cutar coron ya kai 6,159, bayan mutuwar wasu mutane 758 a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata.

Bayanin ya ce 29 daga cikin mutanen da suka mutu a cikin ‘yan sa’oin da suka gabata, ba su fama da wata matsala, inda corona ce ta yi musu farat daya kuma ta yi ajalisu, yayin da shekarunsu sun kama tsakanin 23 ne zuwa 99.

Hukumar lafiya ta duniya WHO bayar da bayanin cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar corona a duniya zuwa yau Talata ya haura 81,000 yayin da wadanda suka kamu da cutar ya haura 1,410,000 a duniya.

Yanzu haka Firayi ministan kasar ta Burtaniya Boris Johnson yana kwance a asibiti a bangaren kulawa ta musamman, bayan da jikinsa ya yi tsanani sakamakon kamuwa da cutar ta corona.


/129