7 Maris 2020 - 06:44
Jagora: Dole Ne Kasar India Ta Dakatar da Kisan Musulman Kasar Da Ake Yi

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’I ya bukaci gwamnatin kasar Indiya ta kawo karshen kissan kiyashin da akewa Musulman kasar, don kada kasashen Musulmi su maida ita saniyar ware.

(ABNA24.com) Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’I ya bukaci gwamnatin kasar Indiya ta kawo karshen kissan kiyashin da akewa Musulman kasar, don kada kasashen Musulmi su maida ita saniyar ware.

Jagoran ya bayyana haka ne a shafinsa na Tweeter da harshen farisanci wadanda kuma aka tarjamasu zuwa harsunan Urdu da kuma turancin Ingilishi, a yau Alhamis.

Ayatullahi Khaminae ya kuma yi Allah wadai da kissan da mabiya addinin Hinbdu sukewa al-ummar Musulman kasar India wanda adadinsu ya kai 40 a cikin kwanaki 4 da suka gabata.

Ya kuma bukaci gwamnatin kasar Indiya ta hana mabiya addinin Hindu masu tsatsauran ra’ayin addini fadawa Musulman kasar. Sannan ya kammala da cewa zuciyan musulmu suna kona saboda ganin yadda ake wa Musulman kasar india kissan kiyashi tun ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Kafin haka dai a ranar Litinin da ta gabata ma, Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr Mohammad Jawad Zarif ya yi kira ga gwamnatin kasar ta Indiya da ta hada kan mutanen kasar ta kuma daina nuna bambanci a cikin mabiya addinai daban-daban na kasar.



/129