(ABNA24.com) Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bayyana wasu akwai sabbin shirye-shiyen gwamnatin kasar na fuskantar kasar Iran, wadanda su ne sabbin takunkuman tattalin arziki, wadanda yake ganin zasu yi wa kasar doka na karshe.
A hirar da ta hada shi da wata mujallar kasar Amurka mai suna “The Washington Free Beacon” Pompeo ya ce Amurka zata maida dukkan takunkuman da aka dorawa kasar Iran a can baya, wanda a fadinsa zai kawo karshen yarjejeniyar Nukliya ta 2015 kwata-kwata.
Pompeo ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zawa ne zai bukaci kwamitin tsaro na MDD ya maida dukkan dakunkuman majalisar wacce aka dorawa kasar ta Iran kafin yerjejeniyar shekara ta 2015.
Sai dai a nan ma sakatarin harkokin wajen na Amurka ya nuna shakkunsa kan samun goyon bayan kasashen turai a wannan bangare.
/129