(ABNA24.com) Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Musawi, ya yi watsi da shiga sharo ba shanun kasar Faransa akan shirin Iran na sararin samaniya da harba tauraron dan adam da kasar ta yi a cikin kwanakin bayan nan.
Musawi ya kara da cewa; Shirin Iran na kera makamai masu linzami ba a yi shi domin ya dauki makamin Nukiliya ba, kuma ba shi karkashin kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231.
Kasar Faransa dai ta soki shirin Iran na fasahar sararin samaniya wanda a karkashinsa ne ta harba tauraron dan adam, a ranar 9 ga watan na na Febrairu.
Musawi ya kara da cewa; Hakkin Iran ne ta ci gaba da ayyukanta a fagen fashar sararin samaniya da kuma bunkasa ayyukanta na ci gaba.
/129
12 Faburairu 2020 - 06:36
Lambar labari: 1009640
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Musawi, ya yi watsi da shiga sharo ba shanun kasar Faransa akan shirin Iran na sararin samaniya da harba tauraron dan adam da kasar ta yi a cikin kwanakin bayan nan.