Ayattullahi Imami Kashani ya bayyana cewa duk wani aiki na tace karfe Uranuim wanda Jumhoriyyar musulnci ta Iran ke bukata, kama daga bangaren amfani da shi wajen kere-kere na’urorin kiyon lafiya, samar da wutar lantari da saurensu wajibi ne a ci gaba da shi kuma wannan hakki ne na Al’ummar Iran, don haka Al’ummar ba za tayi kasa a gwiwa dongane da hakinta.kuma wannan shine abinda jagoran musulnci na Iran Ayyatullahi Ali khaimna’I ke bukata ga tawagar ta Iran.
A yayin da ya koma kan makircin HKI Ayyatullahi Imami ya bayyana cewa kokarin da HKI keyi na mallaka Kasashen Duniya ba za ta cimma kurinta ba har abada kuma rushewarta amfani ga Al’ummar Duniya baki daya ,kamata yayi kasashen yammacin turai su kauracewa HKI domin abittaka da ita babu abinda zai janyo masu inba karin hasara ba.ABNA.