Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

27 Disamba 2024

11:13:26
1517386

Isra'ila Ta Ƙona Asibitin Kamal Udwan

Wakilan gidan talabijin na Aljazeera sun bada rahoton cewa sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kona asibitin Kamal Udwan da ke arewacin zirin Gaza.

Harin da aka kai asibitin Kamal Udwan laifi ne na yaki tare da hadin gwiwar Amurka

Kungiyar Hamas ta sanar da cewa, harin da dakarun yahudawan sahyuniya suka kai a asibitin Kamal Udwan da ke arewacin Gaza, tare da tilastawa ma'aikatan lafiya da marasa lafiya da wadanda suka jikkata da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu barin asibitin karkashin barazanar makamai, bayan da aka kai musu mummunan harin bama-bamai a kewayen Asibitin a daren jiya, wanda ya yi sanadin shahadar mutum sama da hamsin, ciki har da ma'aikatan lafiya biyar, wani laifin yaki ne da ya karu a cikin jerin laifukan da gwamnatin mamaya ta yi kan al'ummar Palastinu.

Kungiyar Hamas ta kara da cewa a cikin wata sanarwa da ta fitar, wadannan laifuka suna faruwa ne a cikin inuwar yin shiru da kuma kasawar kasashen duniya wajen kare fararen hula da cibiyoyin farar hula.

Wannan yunkuri na gwamnatin mamaya na yahudawan sahyoniya da babban mai mara mata baya, gwamnatin Amurka da ke da hannu wajen aikata munanan laifuka a Gaza, tana da cikakken alhakin rayuwar marasa lafiya da wadanda suka jikkata da ma'aikatan lafiya na asibitin bayan katse hanyoyin da suke bi na sadarwa da kafafen yada labarai da buga labarai game da azabtarwa, tsarewa da kuma kai wasu daga cikinsu zuwa wuraren da ba a san su ba.