Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait (AS) -ABNA- ya habarta cewa: ba da dadewa ba Usama Hamdan kakakin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana irin ayyukan leken asiri na kungiyar daular Masarautar a Gaza, sannan kuma masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara da 'Yan jarida masu zaman kansu sun yi nuni da hadin gwiwar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Isra'ila ke yi a kisan kare dangi da suka yi A cikin rahoton faifan bidiyon an ambato a bayan fage na hadin gwiwa tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da Isra'ila kan kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar Palasdinu.
Usama Hamdan ya fada a cikin wannan faifan bidiyo cewa: Hadaddiyar Daular Larabawa ta aike da wata tawagar jami'an leken asiri mai suna Emirates Red Crescent zuwa Gaza domin nemo wuraren da ake harba makaman roka tare da aike da bayanan jami'an nasu zuwa ga yahudawa yan mamaya.
Wannan rahoto ya ci gaba da cewa: Kafin wata ɗan jaridar Faransa ya bayyana kasancewar wata rundunar sojan Hadaddiyar Daular Larabawa a zirin Gaza, wata yar jarida daya ce kawai ta iya shirya rahoto da kanta, kuma ita ce mace mai suna Clarissa Ward, 'yar jaridar CNN. Ta yi amfani da damarta na kasancea tare da daya daga cikin sojojin daular Larabawa a lokacin da yake magana kan matsalolin 'yan jarida na kasashen waje, kuma daya daga cikin 'yan jarida na tashar CLA da ke Tel Aviv ya sanar da kasancewar rundunar sojojin a cikin Gaza.
Bidiyon ya ci gaba da cewa: Ba wani asiri ba ne ai cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta amince fiye da sau daya cewa alakar ta da Isra'ila ta wuce yadda aka saba.
Wani sojan Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce: Ba na jin cewa muna barazana ga Isra'ila, amma na san cewa Isra'ila kawar Amurka ce kamar yadda mu ke kawance da Amurka.
Muhammad Al Khawajah, jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Isra'ila, ya ce wa wani sahyoniya: in Allah ya yarda, ku da mu za mu dawo da karfi a yankin baki daya.
A ci gaba da wannan rahoto; Kasancewarsu a Gaza ba tare da amincewar Hamas ba yana nufin abu daya: Abu Dhabi ta shigarwa yakin Isra'ila kai tsaye da yankin Zirin da al'ummarta.
A ci gaba da faifan bidiyon, Usama Hamdan yana cewa: Hadaddiyar Daular Larabawa kasa ce da ministar harkokin wajenta ke son Isra'ilawa su ci gaba da yaki har sai an ruguza 'Yan Gwagwarmaya musamman Hamas a Gaza.
A cikin wannan faifan bidiyo, wani Bayahuden Isra’ila ya ce, yana mai nuni da Yahudawan da ke kasashen Larabawa; Saboda ana saran sabbin Yahudawa za su zo, ana sa ran su zo su yi sallah tare da mu da sunan Yahudawa, wannan babbar matsala ce, domin za su yi abin da Janar din Isra’ila ko dan kasuwan yahudawan sahyoniya ya ce?
A ci gaba da wannan bidiyon, an gabatar da sakonnin da aka buga akan hanyar sadarwa ta X;
Wani mai amfani mai suna Nora ya rubuta: UAE ita ce babban birni na biyu na wannan muguwar gwamnati bayan Tel Aviv. Sun tabbatar da cewa sun yi yaki a boye da kuma bayyane tare da al'ummar musulmi a kowane wuri.
Wani mai amfani da kafar ya rubuta cewa: A farkon yakin, an yi jita-jita cewa jiragen Emirate za su yi ruwan bama-bamai a Gaza tare da jiragen Isra'ila, abin da ake tsammani kuma ba zai yiwu ba.
Wani mai amfanin da kafar ya rubuta: Allah kar ya bar gwamnatin UAE.
A karshen faifan bidiyon, wani dan kasar Emirate ya ce; Mun san cewa muna alaƙa da ’yan’uwanmu da ke Isra’ila, su ’ya'yan kannen baban nin mu ne, ba ’yan’uwanmu ba.
..........