Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a wata sanarwa da ya fitar bisa zartar da aiwatar da zaben da al'ummar Iran suka yi na kada kuri'a a zaben da ya gabata ya nada Dr. Mas'ud Pezeshkian a matsayin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammadu da alayensa musamman bakiyatullahi a cikin talikai.
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Masani kuma Mabuwayi, wanda ya sake yi wa Iran tagomashin alfahari da daukaka fuskar al'ummarta mai girma; An kammala gagarumin gwajin jarabawar zaben shugaban kasa da kokarin al'umma da jami'ai, cikin mawuyacin hali, cikin natsuwa da nagarta, kuma zababbun al'ummar kasa a shirye suke su sauke nauyi mai girma da ya hau kan su.
Zaben shugaban kasa karo na 14, bayan kammala wa'adin da bai ci ka ba na marigayi shugaba Shahid. ya na daya daga cikin daukakar al'ummar Iran, kuma wata alama ce ta tabbatar da tsayayyen tsarin Musulunci, da ya ke nuni da hankali da wayewar yanayin siyasar kasar. Duba da wasu abubuwa marasa dadi a wasu irin wadannan gwaje-gwajen da suka faru a wasu yankuna na duniya na nuna irin fifikon Iran da Iraniyawa.
A yanzu ina mika godiyata ga dukkan wadanda suka taka rawa wajen samar da wannan karramawa, bisa koyi da abinda al’umma mai girma suka zaba da kaɗa kuri’ar da suka yi wa haziki, mai gaskiya, farin jini, kuma masani Malam Dr. Mas'ud Pezeshkian tare da zartar da shi da nada shi a matsayin Shugaban Jamhuriyar Musuluncin Iran. Ina mai yi masa addu'o'i da fatan samun nasara. Ina tunatar da ku cewa kuri'ar al'umma da zartarwata na za su ci gaba da wanzuwa gareshi matukar dai ya ci gaba da tsare manufofi na bin tafarkin Musulunci da juyin juya hali.
Wassalamu ala Ibadillahil Saliheen
Sayyid Ali Khamenei
7 ga Murdad 1403