Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

8 Mayu 2024

06:26:28
1457040

Manjo Janar Rashid: Idan IRGC Da Sojoji Sukai Aiki Tare, Za’a Gama Da Isra'ila Ta Ƙare Da Aiki Ɗaya Ba Sai Anyi Karo Na Biyu Ba.

“Jiragen Yakin Sojojin Amurka Da Na NATO 240 Ne Suka Taimaka Wa Isra'ila Wajen Kare Harin Ladabtarwa Da Iran Tai Akan Isra’ila. Gwamnatin Yahudawan Sahyoniya Ba Ta Ba Kuskuran Iya Nunawa Duniya Hotunan Illar Harin Na Iran Ba”.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Sardar Gholam Ali Rashid, daya daga cikin kwamandojin Operation "Wa’ad Sadiq": Idan IRGC da sojojin sun kasance a tare, aikin Isra'ila ya ƙare da aiki ɗaya kuma ba sai an ƙara yin na biyu ba.

Janar Gholam Ali Rashid ya ce: "Idan har wani yanayi da kuma yiyuwar sojojin da IRGC su tsaya a gaban sojojin Isra'ila, to za mu gama aikin Isra'ila da wani samame daya kacal, ba kuma za mu kara na biyu ba kamar yadda mu kai a aikin Fathul Mubin daa na Baitul-Maqdis."

I’itimad Jaridar Iran ta yi wata tattaunawa ta musamman da Sardar Gholam Ali Rashid, daya daga cikin kwamandojin da suka gudanar da aikin "Wa’ad Sadiq".

Za Ku Iya Karanta Sassan Wannan Hirar A Kasa Kamar Haka:

Isra'ila ra'ayi tayi kama da wani dashen hakuri ne da likitan hakori yake yi a cikin dasashin mutum wanda kasashen Burtaniya da na Yamma suka shuka, kuma rayuwar Isra'ila ta dogara ga kasashen Yamma. Wato idan wata rana ya zamo babu kasashen  Yamma, Isra'ila za ta ruguje cikin dare, sabanin haka. Wato idan Isra'ila ta ruguje to kasashen yamma ma za su ruguje.

Isra'ila ba ta da ofishin jakadanci a Iran, amma duk ofisoshin jakadancin kasashen yamma na taimaka mata. Suna basu bayanai da duk wani taimako da suke bukata, na siyasa, soja, kafafen yada labarai da dai sauransu.

A baya dai wani dan jarida ya tambayi Amir Mousawi cewa idan yaki tsakanin Iran da Isra'ila ya faru, ta yaya sojojin Iran, IRGC da sojojin Iran za su iya cin galaba a kan Isra'ila? Sa ya mayar da martani da cewa, idan har wani yanayi da yuwuwar hakan ya taso da sojoji da dakarun IRGC suka tsaya a gaban sojojin Isra'ila, to za mu gama aikin Isra'ila da wani samame daya kacal ba tare da karin wasu ayyuka ba daidai gwargwado kamar yadda aka yi a yakin Fathul Mubin da Jerusalem.

Tsawon aikin kwato Khorramshahr ya kai murabba'in kilomita 6000; Wannan yana nufin cewa mun kwato tazarar yankin Falasdinu da aka mamaye a wannan aikin soja.