Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta bisa nakaltowa daga kamfanin dillancin labarai na IRNA cewa: An gudanar da wadannan tarurrukan karar ne a cikin tsari da bukatar Majalisar Dinkin Duniya na karbar ra'ayoyi daga kotun kasa da kasa a birnin Hague game da illolin da ayyukan mamayar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi tun sama da shekaru 75 da suka gabata.
Baya ga koken kungiyar Tarayyar Afirka, kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, za a bincike kan bukatun da kotun duniya ta samu daga kasashe 52 na duniya, wadanda ba a taba ganin irinsu ba a tarihin kotun.
Ayyukan gwamnatin sahyoniyawan da nufin sauya yawan al'umma da kuma matsayin birnin Kudus da ta mamaye, da kuma daukar dokoki na nuna wariya da matakan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta ke yi na daga cikin shari'o'in da ake gudanar da bincike a kansu. .
Isra'ilawa Na Shirin Shafe Falasdinawa Daga Taswirar Duniya
Ministan harkokin wajen Falasdinu a kotun Hague: Sahayoniyawan suna son ruguza al'ummar Palastinu da nuna rashin adalci a matsayinsu na 'yan adam. Suna son a aikata karshen rashin mutuntaka ga al'ummar Palasdinu.
Dole ne Isra'ila ta gaggauta kawo karshen munanan ayyukanta a Gaza
Riyad al-Maliki, Ministan Harkokin Wajen Falasdinu a Kotun Hague: Ina rokon kotun da ta bi ka'idojin kare hakkin bil'adama. Dole ne Isra'ila ta dakatar da duk ayyukanta na tashin hankali a yanzu.