Kamfanin dillancin
labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA ya habarta cewa: Shugaban ya bayyana haka ne a
jawabin da ya yi ga dimbin jama'a a ranar Juma'a a birnin Minab da ke lardin
Hormozgan a kudancin kasar Iran. Shugaban na Iran ya kara da cewa: Mun sha
fadin cewa ba za mu kasance farkon wani yaki ba, amma idan wata kasa ko sojoji
azzalumai na son murkushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka fara kai mata yaki,
to kuwa za a mayar da martani mai tsanani.
Ya ce karfin sojan Iran ba komai ba ne ga kasashen yammacin Asiya, sai dai tushen tsaro ne da kasashen yankin za su dogara da shi.
Shugaban ya ce makiya suna amfani da harshen barazana ga Iran, har ma ya ce zabin soja yana kan teburi, amma a yanzu suna sanar da cewa ba sa son a yi arangama da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaban ya jaddada cewa karfin soji na Iran na da nufin kare kansa da kuma dakile makiya.
Shugaban kasar Iran ya yi ishara da nunin baje kolin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da ya ziyarta da sanyin safiyar jiya inda ya ce makiya ba za su iya jurewa irin sabbin abubuwa da masana Iran suka yi ba, a 'yan kwanakin nan dai jami'an Amurka sun yi magana kan shirin kafa wata sabuwar dabarar jerin hare-hare kan muradun Iran a Iraki da Siriya a matsayin martani ga harin da aka kashe sojojin Amurka uku a Jordan a makon jiya. Shugaban Amurka Joe Biden ya zargi kungiyar da ya kira "kungiyoyi masu samun goyon bayan Iran" wadanda galibinsu ke da sansani a Iraki da kai hari wanda ya kuma raunata akalla sojoji 34.
Iran dai ta musanta cewa tana da hannu ta kowace fuska da hare-haren da ake kaiwa sojojin Amurka a yankin, sannan ta ce kungiyoyin 'yan gwagwarmaya ba sa karbar umarni daga Tehran, haka kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta da wata rawa a cikin hukuncin da suka yanke na daukar matakan ramuwar gayya na kare kai wa al'ummar Palasdinu.