Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

7 Satumba 2023

12:21:29
1391827

An Kafa Tarihin Arbaeen Bana Da Zuwan Maziyarta Miliyan 4 Daga Iran Ta Kan iyakokin 'Yan Kasar Waje

Al'ummar Kasashe 10 Ne Suka Halarci Taron Arbaeen A Iraki Daga Iran

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Sardar Ahmadreza Radan ya bayyana a kan iyakar kasar Chazaba, yayin da ya ke tsokaci kan ziyarar da ya kai dukkan iyakokin kasar, inda ya ce: A yayin taron Arbaeen na bana, adadin maziyarta da suka bar kasar ya zarce miliyan 4, kuma an karya tarihin na tsawon shekaru kuma ind aka kafa tarihi A bana, baya ga sauri da daidaito wajen ba da hidima ga magoya bayan Husaini da magoya sahabbansa, an kafa tarihin maziyarta na shekara-shekara.

Ya kara da cewa: “A cikin wadannan hanyoyi mun shaida cewa duk mai kowane harshe da kowace kabila zuciya daya ce garesu wajen nuna soyayyar Aba Abdullah Al-Husain, kuma wannan tausasawa da sada zumunci yana tunatar da mu ranakun kariya mai tsarki da kuma Tawassuli ga Aba Abdullahi."