Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

6 Satumba 2023

15:58:26
1391661

An kammala taron Tattakin Arba'in na shekarar bana ta 1445/2023 a Abuja Lami lafiya. Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Yau Laraba 20 ga watan Safar ta dace da ranar arba'in na Imam Husaini (a.s), wanda kuma a Yau ne ƴan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky (H) su ka kammala tattakin arba'in na Imam Husaini (a.s), wanda aka soma gabatarwa tun a ranar 16 ga watan Safar har ya zuwa Yau Laraba 20 ga watan Safar wacce ranar kuma ta dace da ranar da Imam Husaini (a.s) jika a gurin Ma'aiki (S) ke cika kwanaki arba'in da kisan gillar da aka masa a ranar 10 ga watan Almuharram shekara ta 61 bayan hijira.

Tattakin ya gudana ne a duk faɗin ƙasarnan wanda aka soma tun a matakin zanguna da suka haɗa da, Zangon Kano, Kaduna, Funtua, Fambeguwa, Suleja, Maraba, wanda a ƙarshe Yau aka haɗu baki ɗaya a babban birnin tarayya Abuja aka gabatar taron na arba'in.

An gudanar da tarukan kashi biyu duk a cikin babban birnin tarayya Abuja, wanda kashi na farko an fara shi ne daga Wuse zuwa Bega da misalin ƙarfe 8 na safe kashi na biyu kuma an fara da misalin ƙarfe 10 na safe, daga Kubuwa Arab Junction zuwa NNPC.

Sheikh Abubakar Maina ne ya gabatar da jawabin rufe tattakin inda a cikin jawabin da ya gabatar a gurin ya bayyana dalilin fitowar ta Yau inda yake cewa, “mun fito ne domin jajantawa Annabi (S) na abin da ya samu jikansa a Karbala, mu muna tare da Ahlulbaitii (a.s) kuma mun yi tawaye ga waɗanda suka yi musu tawaye, arba'in yana da muhimmanci sosai a musulunci, daga cikin alamomin mumini akwai ziyarar arba'in.”

Haka kuma Malamin ya yi kira ga ƴan'uwa da su sanya Imam Husaini (a.s) a matsayin madubinsu a cikin kowane al'amari.

Ya cigaba da cewa, “dalilin da ya sa Manzon Allah (S) ya sanya Imam Husaini ya zama alami shi ne, su taurari ne su manara ne na haske, Manzon (S) ya ce, 'Husaini misbahulhuda wa safinatunnaja' ma'ana Imam Husaini fitila ne na haske kuma jirgin tsira.”

Tattakin ya gudana lafiya. 6/9/2023.