Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

9 Mayu 2023

22:16:36
1364267

Daidaita Dangantaka Da Tsakanin Saudiyya Da Isra'ila A shekarar 2023 Abu Ne Mai Wuya

Hukumar gidan radiyo da talabijin ta Sahayoniyya (KAN) ta sanar da hakan cewa: Da wuya Isra'ila za ta iya shawo kan Saudiyya ta daidaita dangantakarta a shekarar 2023.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa,

A cewar rahoton na wannan kungiya, a yau ne ministan harkokin wajen gwamnatin sahyoniyawan Eli Cohen zai gana da takwaransa na Amurka Anthony Blinken ta wayar tarho, kuma abunda ak shirya shine bangarorin biyu su tattauna kan kokarin daidaita alakar dake tsakanin Tel. Aviv da Riyadh yayin tattaunawa ta wayarsu tarho.