Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

2 Mayu 2023

13:31:07
1361999

Jihadul Islami: Dukkan Hanyoyin Zabi Don Mayar Da Martani Ga Laifin Kisan Shahida "Adnan" Abude Suke

Babban magatakardar Harkar Jihad Islami ya bayyana cewa, mun zabi tafarkin shahada ne da son ranmu, ya kuma bayyana cewa ba za mu yi watsi da tafarkin jihadi da gwagwarmaya ba, har sai an kwato kasarmu daga hannun makasa yahudawan sahyoniyawan dake kisa da aikata muggan laifuka.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul Bait (A.S) - ABNA- ya habarta cewa, Ziyad Al-Nakhleh, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palastinu a ranar Talata, ya shaida cewa shahadar "Khidr Adnan daya daga cikin fursunan Palastinu, kuma daya daga cikin jagororin kungiyar Jihadil Islama na Palasdinawa wanda ya yi shahada a gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila bayan shafe kwanaki 86 na yajin cin abinci ya mayar da martani tare da sanar da cewa mun zabi tafarkin shahada da yardarmu sannan Sheikh Khizr Adnan shi ma ya zabi wannan zabin tafarki.


Babban sakataren kungiyar Jihadi Islami ya kara da cewa: Duk ranar da ta zo a tarihin al'ummarmu ta tabbatar da cewa nasararmu za ta zo da izinin Allah. Wasiyyar da Sheikh Adnan ya yi a cikin dogon yakin, fuskantar makiya kai tsaye da kuma shahadarsa mai girma, wata lambar girmamawa ce a kirjin al'ummar Palastinu.


Ziyad Al-Nakhleh ya ci gaba da cewa: Ci gaba da gwagwarmaya da tsayin daka da jajircewa kan hakkinmu na Palastinu shi ne taken Jihadinmu wanda ba zai tsaya ba saboda sadaukarwa, kuma wannan shi ne aikinmu na ci gaba fiye da kowane lokaci.


Babban magatakardar Harkar Jihad ya ci gaba da cewa: A yau muna biyayya ga dukkanin shahidai da Sheikh Khizr Adnan da wadanda za su shiga cikin dimbin shahidai tsarkaka, kuma ba za mu bar tafarkin jihadi da tsayin daka ba har sai an 'yanto kasarmu daga hannun makasa yahudawan sahyoniya da ke aikata laifuka.


Ya kara da cewa: Mu sauke nauyin da Allah ya dora mana na 'yantar da Kudus da Palastinu da kuma korar makiya masu kisa daga kasarmu.


.........................