Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

12 Satumba 2022

18:13:59
1305297

An Ayyana Hutu A Karbala Daga Lahadi Har Zuwa Alhamis

An Ayyana Hutu A Karbala Daga Lahadi Har Zuwa Alhamis

Gwamnatin Birnin Karbala Ta Ayyana Ranar Lahadi Zuwa Alhamis A Matsayin Hutu A Ranekun Arbaeen Na Imam Hussain (AS).

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya nakalto maku cewa, Gwamnatin Birnin Karbala ta bayyana ranar Lahadi zuwa Alhamis a matsayin ranar hutu domin ranar Arbaeen na Imam Hussain (AS).


Ofishin yada labarai na "Nasif al-Khattabi" gwamnan Karbala ya fitar da wata sanarwa da ke cewa: Domin aiwatar da tsare-tsaren tsaro da hidima da bude kofa ga al'ummar kasa mai tsarki na Karbala domin karbar miliyoyin maziyartan Imam Hussaini (a.s), an yanke hukunce yin hutun gida a cikin ranekun Arbaeen.


Sanarwar ta ci gaba da cewa: Wannan hutun ya fara ne a ranar Lahadi 11 ga watan Satumba (20 ga Shahrivar 1401) kuma za a ci gaba da shi har zuwa ranar Alhamis 15 ga Satumba (24 ga Shahrivar 1401hs), amma wanna hutun ban da ma'aikatan gwamnatin Karbala da dukkan cibiyoyin tsaro da na hidima.


Ya kamata a lura cewa a bana Arbaeen Husaini zai kasance ranar Asabar 26 ga watan Shahrivar wato 17 ga watan satumba 2022 kuma tuni miliyoyin maziyartan gida da na waje suka tashi zuwa wannan birni.