(ABNA24.com) A Aljeriya, yau Alhamis ne ‘yan kasar ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar, watanni takwas bayan murabus din shugaba Abdelaziz Buteflika sakamakon matsin lamba na masu bore.
‘Yan takara biyar ne ke fafatawa a zaben, wanda shi ne na farko tun bayan Shugaba Buteflika mai murabus da ya kwashe shekaru ashirin kan madufun ikon kasar.
Kimanin ‘yan Aljeriya miliyan 24 ne aka kiyasta zasu kada kuri’a a zaben, saidai kusan rabinsu na masu kin jinin zaben wanda suke ganin cewa tamakar ci gaban tsohuwar gwamnatin kasar ne, saboda galibin ‘yan takaran sun taba samun kusanci da tsohuwar gwamnati.
‘Yan takaran dake fafatawa a zaben, sun hada da Abdelaziz Belaïd, wanda shi ne mafi kankanin shekaru daga cikinsu, sai sauren da suka had da Talai el Houriat da Abdelkader Bengrina da Azzedine Mihoubi da kuma Abdelmadjid Tebboune, wandanda duk sun taba rike mukamin minista a lokacin gwamnatin shugaba Buteflika.
An dai shafe watannin da dama ana zanga zangar kin jinin zaben na ranar 12 ga watan Disamba.
/129
14 Disamba 2019 - 04:48
News ID: 993508

A Aljeriya, yau Alhamis ne ‘yan kasar ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar, watanni takwas bayan murabus din shugaba Abdelaziz Buteflika sakamakon matsin lamba na masu bore.