13 Nuwamba 2019 - 06:06
Jordan Da Sudan Suna Karya Takunkumin Sayarwa Libya Makamai

Majalisar dinkin duniya ta bada rahoton cewa kasashen Jordan da hadaddiyar daular Larabawa da kuma Turkiyya suna karya kudurin day a hana sayarwa kasar Libya makamai.

(ABNA24.com) Majalisar dinkin duniya ta bada rahoton cewa kasashen Jordan da hadaddiyar daular Larabawa da kuma Turkiyya suna karya kudurin day a hana sayarwa kasar Libya makamai.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya sami kofin rahoton kwamitin da ke sanya ido na majalisar a kan tabbatar da haramcin sayarwa kasar ta Libya makamai.

Rahoto ya kara da cewa shishigin da wadannan kasashe suke yi a kasar ta Libya ya kai ga wasu jiragen saman yaki na kasashen waje sun yi sanadiyyar mutuwar yan gudun hijira a kasar ta Libya.

Har’ila yau rahoton ya zargi kasar Sudan, musamman Mohammad Hamdan Dagalo shugaban wata rundunar sojojin kasar ta Sudan da aika sojojin kimani 1000 zuwa kasar ta Libya. Amma wasu majiyoyin gwamnatin Sudan sun musanta wannan zargin.




/129