13 Nuwamba 2019 - 06:06
​Iran Za Ta Ci Gaba Da Mutunta Yerjejeniyar Nukliyar Kasar Ta Shekara Ta 2015

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasar Iran za ta ci gaba da mutunta yerjejeniyar Nukliya ta shekara ta 2015, don amfanin da kasar zata samu a cikinta.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasar Iran za ta ci gaba da mutunta yerjejeniyar Nukliya ta shekara ta 2015, don amfanin da kasar zata samu a cikinta.

Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a garin Kermon inda yake ziyarar aiki a jiya Litinin. Rouhani ya kara da cewa a shekara mai zuwa kasar zata amfana da kudurin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya na yerjejeniyar nukliyar mai lamba 2231, wanda ya bawa kasar damar saya da sayar da makamai, da kuma wasu al-amuran na siyasa da tattalin arziki.

Kafin haka dai akwai wasu kudurorin Majalisar wadanda suka hana kasar damar yin hakan.

Shugaban ya kara da cewa kasar Iran a halin yanzu ta dauki matsayin tsaka-tsaki, a bangare guda za ta ci gaba da jingine yerjejeniyar, sannan ba zata fice gaba daya ba, don amfanin da zata samu a cikinta, gwagwadon maslahar kasar.




/129