(ABNA24.com) A Iraki, mutane 12, aka rawaito cewa sun rasa rayukansu, a wani harin bam da aka kai cikin motar bus, a daidai wata gada a shiga Kabala, birni mai tsarki na mabiya mazahabar shi’a a Iraki.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai wasu biyar da suka raunana kamar yadda wata majiyar soji ta shaidawa manema labarai.
Rahotanni daga kasar sun ce mafi yawa wadanda lamarin ya rusa dasu yara ne da mata .
Babu dai wata kungiyar data dauki alhakin kai harin.
tun dai bayan murkushe kungiyar IS a Iraki a cikin shekara 2017, ba’a cika samun hare hare a birnin na Karbala ba, saidai har yanzu akwai wasu tsagerun ‘yan kungiyar da’esh dake kai hare hare a wasu yankunan kasar.
/129
22 Satumba 2019 - 04:47
Lambar labari: 977086
A Iraki, mutane 12, aka rawaito cewa sun rasa rayukansu, a wani harin bam da aka kai cikin motar bus, a daidai wata gada a shiga Kabala, birni mai tsarki na mabiya mazahabar shi’a a Iraki.